Hukumomi a kasar Saudiyya sun karawa Najariya yawan kwanakin kammala jigilar Alhazai daga ranar 4 zuwa 6 ga watan Yuli.
Kakakin hukumar aikin hajji ta kasa, Fatima Usara ce ta bayyana haka ga manema labarai.
Tace an samu tsaiko wajan jigilar alhazanne saboda soke tafiye-tafiyen jiragen sama da aka yi dalilin gurbatar yanayi.