Kasar Saudiyya ta yi Allah wadai da kisan da kasar Israela kewa Falas-dinawa.
Ta bayyana cewa Israelan nawa Falas-dinawan kisan kare dangi.
Israela ta kashe mutane akalla 21 a harin data kai kan al-Mawasi dake Rafah.
Hakan ya zo ne bayan da ta kashe mutane sama da 40 a harin data kai kan wani sansanin a Rafah ranar Labadi.
Ma’aikatar harkokin waje ta Kasar Saudiyya tace Israela ce ke da alhakin koma menene ke faruwa a Rafah.
Kuma ta yi kiran kasashen Duniya da su dauki matakin hana wannan kisa da Israela kewa Falasdinawan.