Kasar Thailand ta halatta noma da mallakar tabar wiwi da kuma amfani da ita a cikin abinci da magunguna.
Kasar itace kasar Asia ta farko data halatta amfani da tabar ta wiwi.
Saidai tace shan tabar wiwin dan kawai a bugu ya sabawa doka.
Tuni dai gwamnatin kasar ta bayyana cewa zata fara rabawa manoma irin tabar wiwin da za’a fara nomawa a kasar.