fbpx
Thursday, August 11
Shadow

Kasashen Afirka na nazari kan rufe iyakokin Najeriya

Shugabannin kasashen kungiyar hadin kan Afirka ta AU sun kafa wani kwamiti da zai duba sannan ya hada rahoto game da yadda Najeriya ta garkame iyakokinta na kasa tsakaninta da makwabtanta.

Kamfanin dillancin labarai na NAN ya ruwaito Garba Shehu, mai magana da yawun gwamnatin Najeriya yana cewa an yanke shawarar ne a daren ranar Lahadi yayin taron kungiyar ta AU a Addis Ababa, babban birnin Habasha wato Ethiopia.
Garba Shehu ya bayyana hakan ne ranar Litinin, inda ya ce kwamitin zai yi aiki ne karkashin jagorancin shugaban kasar Burkina Faso, Roch Marc Christian Kabore.
Ministan harkokin wajen Najeriya, Geoffrey Onyeama, ya shaida wa ‘yan jarida bayan taron cewa Shugaba Muhammdu Biuhari ya halarci taron, wanda shugaban AU, Shugaba Mahamadou Issoufou na Nijar ya jagoranta.
Kazalika Garba Shehu ya ce shugabannin sun tattauna kan sabon kudin Eco na kasashen Afirka ta Yamma da kuma yanayin da ake ciki a kasar Guinea Bissau bayan kammala zaben shugaban kasa.


(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});

Karanta wannan  Majalissar dinkin duniya tace harkar Crypto zata iya rusa Najeriya da sauran kasashen da suka cigaba


(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});

Ku biyomu a shafukanmu na sada zumunta dan samun labarai masu kayatarwa:

A shafin twitter zaku same mu a @hutudole

A shafin Facebook zaku samemu a @hutudolehausa

Danna nan dan sanin yanda zaku tallata hajarku a shafin hutudole

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Leave a Reply

Your email address will not be published.