A yayin sa al’ada da addimi yawanci ansan maza ne ke auren mata fiye da daya. Akwai kasashen Duniya da suka halattawa mace ta auri maza da yawa.
Kasar India.
Akwai yankuda da yawa a kasar Indiya dake amincewa mata auren maza fiye da daya, wasu daga cikinsu sune:
Jaunsarbawar
Akwai kuma kabilar Nilgiris data Najanad Vellala da suma ke wanan kazantar, hakanan a Tibet ma an samu mata masu auren maza fiye da daya.
Kenya.
A kasar Kenya ma an samu rahotannin auren maza fiye da daya da mata keyi.
An samu rahoton farko ne a shekarar 2013. Inda kuma daga nan kofa ta bude.
Kasar China.
A kauyukan kasar China an samu rahotannin mata na auren maza da yawa, saidai wannan al’ada ba a yinta a biranen kasar.
Nepal.
Kasar Nepal ma na cikin kasashen da ake wannan bakar al’ada, duk da hukumomi a kasar sun haramta hakan amma ‘yan kasar da dama suna yi.
Gabon.
Kasar Gabon ma na cikin kasashen da aka samu rahoton bullar wannan al’ada.