fbpx
Thursday, August 18
Shadow

Kasashen Duniya na ta mamakin yanda aka sace daliban Jangebe

Najeriya na ci gaba da fuskantar matsin lamba daga kasashen duniya, kwana daya bayan sace ‘yan mata sama da 300 daga wata makarantar kwana a jihar Zamfara dake arewacin kasar.

Majalisar Dinkin Duniya, tare da gwamnatocin Amurka da na Ingila sun bayyana harin da aka kai a makarantar sakandaren ‘yan mata da ke Jangebe a matsayin abin ban tsoro tare da yin kira da a sake su ba tare da bata lokaci ba.

Kamar a 2014 lokacin da aka sace yan matan sakandiren Chibok, a wannan karon ma gwamnati na fuskantar matsin lamba don ganin an sake sakin wasu gungun yara ‘yan makaranta da aka sace.

Yawancin waɗannan ƙasashe na mamakin yadda har za a iya sace mutum sama da 300 a kama hanya a tafi da shi ba tare da jami’an tsaro sun kai ɗauki domin daƙile abin da ake shirin aikatawa ba, ko da yake a Najeriya, wannan abu ne da ya sha faruwa.

Mutane da dama na fargabar cewa faruwar wannan al’amari da ma irinsa da suka faru a baya, zai iya sa iyaye su daina tura yaransu makaranta domin kare lafiyarsu.

Da yake maida martani game da satar, Sakatare Janar na Majalisar Dinkin Duniya Antonio Guterres ya kira hare-hare a kan makarantu a matsayin mummunan take hakkin dan adam.

Gwamnatin Burtaniya ta ce dukkan yara sun cancanci samun damar neman ilimi hankali kwance, sannan ministan Burtaniyan kan harkokin Afrika James Duddridge ya ce kasarsa na aiki kafada da kafada da Najeriya don taimakawa yara mata su sami ilimi ba tare da wata fargaba ba.

A nata bangaren, Amurka ta yi kira da a tabbatar da hukunta wadanda ke da alhakin sace daliban.

Jakadiyar Amurka a Majalisar Dinkin Duniya Linda Thomas-Greenfield ta bukaci cewa dole ne a mayar da ‘yan matan ga danginsu nan take.

Duk wannan na faruwa ne bayan ceto wasu dalibai 42 da ma’aikatan Kwalejin Kimiyya ta Gwamnati da ke Jihar Neja daga wadanda suka yi garkuwar da su a ranar Asabar.

An dauke su kusan makonni biyu da suka gabata, kuma sun shafe fiye da mako guda kafin a kai ga sakinsu.

Hotunan bidiyon da aka watsa a shafukan sada zumunta a Najeriya bayan sako su, sun nuna su cikin jigata da kuma mummunan yanayi.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Leave a Reply

Your email address will not be published.