fbpx
Wednesday, March 29
Shadow

“Kasashen Duniya suna girmama shugaba Buhari, Ba’a hanashi shiga Amurkaba,”>>Femi Adesina

Me baiwa shugaban kasa shawara ta fannin watsa labarai Femi Adesina ya musanta maganar da tsohon mataimakin shugaban kasa, Alhaji Atiku Abubakar akan shugaban kasa Muhammadu Buhari cewa wai kasar Amurka ta hanashi shiga kasar tun shekaru goma shabiyar da suka gabata.

A wata hira da sanannen dan jaridarnan, Dele Momodu yayi da Atikun, ya tambayeshi dalilin dayasa baya shiga kasar Amurka, ana kishin-kishin din cewa jami’an kasar suna nemanshi ruwa a jallo,.

Kada bakin da zaiyi sai yace, yana shiga kasashen turai kuma ya fito lafiya kuma babu wanda ya taba yunkurin kamashi, ya kara da cewa ai shugaban kasa Muhammadu Buhari shima kasar ta Amurka na nemanshi tun shekaru shabiyar da suka gabata amma gashi daya zama shugaban kasa yana shiga kasar babu shamaki, haka kuma Atikun yace firaiministan kasar Indiya Shima kasar Amurka na nemanshi amma daya zama shugaban kasa gashi yana shiga kasar babu shamaki.
Femi Adesina ya bayyana cewa, ba kasar Amurka kawaiba, mafi yawancin kasashen Duniya na girmama shugaban kasa Muhammadu Buhari, tun kamin ya zama shugaban kasa da kuma yanzu da ya zama shugaban kasar, mutumne da aka sanshi da gaskiya da rikon amana kuma ba’a hada baki dashi ayi cin hanci.
Adesina ya kara da cewa, maimakon Atikun ya kakaro wannan magana da ba gaskiya bace ya fada, kamata yayi lokacin da aka tambayeahi meya hanashi shiga kasar ta Amurka ya fito ya fadi gaskiya, kuma ya mayar da hankali wajan warware maysalar data hanashi shiga kasar.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Talla: Danna nan dan samun gagarumar kyauta

Karanta wannan  NDLEA ta kama yaya da kanwarta da Wiwi a Katsina

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *