Gwamnatin tarayya ta bayyana cewa kashi saba’in bisa dari na magagungunan da ake amfani dasu a kasar Nakeriya daga waje ake shigo dasu,
Sabda haka yanzu tana kokarin yin maja da kasar Cuba domin a rage kashi 20 cikin 70 din.
Shugaban kungiyar NABDA ta fasahar kere-kere ta bangaren magunguna a Najeriya, farfesa Mustapha Abdullahi ne ya bayyana ne a hakan babban birnin tarayya Abuja.
Kuma yace kudin Najeriya zai kara daraja a idon Duniya idan aka kaddamar da wannan abin.