Tun bayan da jita-jitar tsayar tsohon shugaban kasa, Goodluck Jonathan takarar shugaban kasa a shekarar 2023 ta bayyana, sai aka fara samun cece-kuce tsakanin ‘yan Najeriya.
Wasu suna goyon bayan hakan yayin da wasu kuma ke cewa ya kamata Goodluck Jonathan ya hakura da takara.
Ana tunanin dai Goodluck Jonathan zai bar jam’iyyar PDP ya koma APC a matsayin wani bangare na shirin tsayawa takarar a shekarar 2023.
Hakanan kuma Goodluck Jonathan akai-akai yana yawan zuwa ganawa da shugaban kasa, Muhammadu Buhari.
Saidai Jonathan tuni ya musanta wannan jita-jita.