Gwamnan jihar Kano, Dr. Abdullahi Umar Ganduje ya gabatar da hotunan sabuwar gadar da zai gina a kwanar Hotoro, NNPC dake Kano.
Gadar zata kasancene akwai ta kasa data sama. Ya gabatar da hotunan gadar ne wanda za’a sakawa sunan shugaban kasa, Muhammadu Buhari ga majalisar zartaswa ta jihar dan amincewa.
Hadimin gwamnan, Abubakar Aminu Ibrahim ne ya bayyana haka ta shafinsa na sada zumunta.







