Sanata Shehu Sani ya gayawa Gwamnan Neja Sani Bello da yayi amfani da wannan damar wajen gyara makarantar GSC Kagara, duba da yadda aka nuna hotunan makarantar bayan an sace wasu dalibai.
Wannan yana kunshe ne a cikin wani sako da Shehu Sani ya wallafa a shafinsa na Twitter.
Ga sakon kamar haka:
“Wani lokaci, wasu musibu sukan zama sanadiyyar gyara ga wasu abubuwa, kayi amfani da wannan damar wajen gyara makarantar GSC Kagara. Rashin zageye makarantar da kyau ya taimaka wajen satar daliban kuma abun kunya ne a ga makarantar Gwamnati a ya mutse.”