A ranar Talata ne kungiyar dattawan Arewa ta bukaci shugaban kasa, Muhammadu Buhari ya yi murabus saboda gazawa wajen samar da tsaro a kasar.
Kungiyar ta gabatar da bukatar ne a cikin wata sanarwa da kakakinta, Dr Hakeem Baba-Ahmed ya fitar.
Ya ce abin takaici ne yadda bayan shafe kusan shekaru bakwai yana mulki har yanzu Buhari bai da amsa kan kalubalen tsaro a fadin kasar nan.
Sanarwar ta ci gaba da cewa, “Gwamnatin shugaban kasa Muhammadu Buhari ba ta da amsoshi kan kalubalen tsaro da muke fuskanta.
Ba za mu iya ci gaba da rayuwa da mutuwa a ƙarƙashin umarnin masu kashe mutane, masu garkuwa da mutane, masu fyade da ƙungiyoyin masu laifi iri-iri waɗanda suka tauye mana haƙƙinmu na rayuwa cikin aminci da tsaro.