Dan takarar shuganam kasa na jam’iyyar APC, Bola Tinubu ya karyata babban abokin hamayyarsa dan takarar PDP wato Atiku kan batun da yayi akansa ranar juma’a.
A ranar juma’a ne Atiku yace Tinubu dama akidar shi ce tsayar da Musulmi da Musulmi a matsayin ‘yan takarar shugaban kasa.
Inda ya kara da cewa a shekarar 2007 ma lokacin suna jam’iyyar AC Tinubu ya nemi shi cewa zabe shi a matsayin abokin takarar shi amma yaki saboda su Musulmai ne.
Amma yanzu hadimin Tinubu Tunde Rahma ya karyata hakan inda yace karya Atiku keyiwa uban gidansa, shi da kanasa ya nemi Tinubu daya amince ya zama abokin takararsa.