fbpx
Tuesday, July 5
Shadow

Kerala wani yanki a kasar Indiya da ake musu ruwan sama mai kama da launin Jini

Allah Mai Iko.

Tarihi ya tabbatar da cewa an samu zubar ruwan sama mai kama da launin jini a wani yanki mai suna kerala dake kasar Indiya.

A wani binciken Masana da suka gudanar sun bayyana  cewa hakan na faruwa ne idan abubuwan da iska ke fitarwa ya hade da damshi damshin dake cikin gajimare.
“Idan abubuwa masu launin ja dake cikin kasa suka gauraya da wannan gajimare sai launin ruwan sama mai launin jini ya samu”.
Tarihi ya nuna cewa an samu zubar ruwan saman mai kama da launin jini a lokuta daban-daban kamar a shekarar Alif 1896, da kuma shekarar 2001, da 2012.
Bayanan da Masana kimiyya su ka yi ya zo dai dai da lamarin da ya faru a watan Juli a shekarar 2018 a kasar Rasha inda aka samu ruwan sama mai launi ja, a wani birni mai suna Norilsk.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Karanta wannan  Kalli Bidiyo: An saka dokar hana tadi da 'yan mata a mota me tinted a Kaduna: An ce za'a zane duk yarinyar da aka kama

Leave a Reply

Your email address will not be published.