fbpx
Thursday, August 18
Shadow

Kevin De Bruyne zai cigaba da taka leda a kungiyar Manchester City>>Pep Guardiola

Kocin kungiyar Manchester City, Pep Guardiola ya bayyana cewa Kevin De Bruyne zai cigaba da taka leda a kungiyar duk da cewa manema labarai da dama sun bayyana an samu tangarda a cikin yarjejeniyar kwantirakin dan wasan.

Kwantirakin Kevin De Bruyne ba zai kare ba har sai nan sa shekara ta 2023 amma har kungiyar City ta yiwa dan wasan tayin sabunta kwantiraki wanda har yanzu bai rattaba hannu ba saboda yaji kunya duba da kungiyar bata kara mai ko sile ba a cikin albashin sa na yuro 280,000 a kowane mako.

Karanta wannan  Manchester United zata dauki Casemiro daga Real Madrid

Kevin De Bruyne yayi nasarar lashe kyautar dan wasan PFA na kakar data gabata, saboda haka ne yake so kungiyar ta sabunta mai kwantiraki bisa matsayin shi na daya daga cikin zakarun yan wasan tsakiya na tarihi kuma mataimakin kaftin din Mancheatwr City.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Leave a Reply

Your email address will not be published.