fbpx
Wednesday, August 10
Shadow

Kimanin mambobin jam’iyyar PDP 18,000 ne a jihar Oyo suka koma jam’iyyar APC.

Da Duminsa: Mambobin PDP 18,000 sun koma APC a Oyo

A karkashin jagorancin dan majalisar wakilai mai wakiltar mazabar Ibarapa ta tsakiya/Ibarapa ta arewa, Muraina Ajibola, masu sauya shekar sun samu tarba daga shugaban jam’iyyar APC Isaac Omodewu, dan takarar Sanatan Oyo ta kudu, Sarafadeen Alli da sauran shugabannin jam’iyyar.

A wajen taron akwai mataimakin shugaban jam’iyyar Alhaji Olaide Abas da tsohon sakatare Mojeed Olaoya da sauran shugabannin jam’iyyar a Ibarapaland.

Ajibola ya yi alfahari da cewa yana da mabiya kimanin 18,000 da suka zo tare da shi APC, kuma ya roki ‘yan kungiyar da kada su bar jam’iyyar ga masu zuwa su shiga.

Karanta wannan  Wata sabuwar annoba ta sake barkewa a kasar Chana

Omodewu ya ce ya dade yana kira ga ‘ya’yan jam’iyyar da suka yi korafin kuma korafin ya bada sakamakon mai kyau. Ya kuma yi maraba da wadanda suka sauya sheka, inda ya ce za su hada kai don kayar da gwamnatin PDP.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Leave a Reply

Your email address will not be published.