Kimanin mutane goma ne ke mutuwa sanadiyyar cutar Maleria a kowace ‘awa guda a Najeriya, ma’aikatar kiyon lafiya ta jihar Adamawa ta bayyana.
Ministan kiwon lafiya na jihar, Abdullahi Isa ne ya bayyana hakan inda yace mutane 90,000 ne ke mutuwa sanadiyyar cutar a kowace shekara a Najeriya.
Ya kara da cewa cutar ta addabi Duniya bakidaya, amma tafi yawa a Afrika, kuma Najeriya nada kashi daya bisa hudu na cutar.