fbpx
Wednesday, August 10
Shadow

“Kiran da aka yiwa gwmnati ta soke kungiyar malamai ta ASUU shirme ce”>>Malamin jami’ar Port Hacourt

Tsohon shugaban kungiyar malaman jami’o’in Najeriya na jihar Port Harcourt, Dr Austen Sado ya bayyana cewa kiran da aka yiwa gwamnati ta soke kungiyarsu shirme ne.

Daya daga cikin masu fada aji na jam’iyyar APC, shugaba Sam Nkire ne ya bukaci gwamnatin tarayya data soke wannan kungiyar ta malaman jami’o’in Najeriya,

Inda yace yajin aikin da suke yi na jawa kasa cibaya sosai kuma ba karamin abu bane.

Amma tsohon shugaban kungiyar malaman , Sado ya bayyanawa manema labarai na Punch cewa yayi mamakin jin irin wannan maganar daga bakin shugaban jam’iyya, kuma wannan maganar shirme ce saboda gwamnatin ce ta kawo matsalar.

Leave a Reply

Your email address will not be published.