fbpx
Monday, March 1
Shadow

Kiran gwamna Bala Muhammad da Dan ta’adda ba daidai bane>>FFK ya gayawa Gwamna Ortom

Tsohon Ministan Sufurin jiragen sama,  Femi Fani Kayode ya mayarwa gwamnan jihar Benue, Samuel Ortom martani kan kiran Gwamnan Bauchi da yayi a matsayin dan ta’adda.

 

Gwamna Ortom ya zargi Gwamnan Bauchi da goyon bayan ta’addanci inda yace ya shirya sa Fulani su kasheshi.

 

Saidai FFK yace gwamnan Bauchi mutum ne da baya nuna kabilanci ko banbancin addini, yace watakila ba dan shi ba da Goodluck Bai zama shugaban kasar riko ba.

 

Yace shine a wancan lokacin ya rika kokari a majalisa wajan ganin an baiwa Jonathan Mulkin rikon kwarya. Yace dan haka kiransa da dan ta’adda ba daidai bane.

 

”He is a  leading member of the PDP Ministers Forum, a group which I belong to, and I assure anyone that cares to listen that he is far more comfortable with indulging in an intellectual joust in which we can agree to disagree than in carrying guns, throwing bombs and killing people. It would serve our interest better if we learnt to separate the wheat from the chaff and stop demonising people simply because they do not share our views.

 

”To call Bala a terrorist is unacceptable and erroneous. I doubt that he has ever killed a chicken let alone a human being” Fani-Kayode concluded.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:


×
Kano

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *