fbpx
Thursday, June 30
Shadow

Kisan Anambra: ‘Saura kadan na haukace bayan kashe min matata mai ciki da ‘ya’yana huɗu’

Mutumin da aka kashe wa matarsa mai ciki wata tara da kuma ƴaƴansa huɗu a jihar Anambra a kudancin Najeriya, ya ce ya ji kamar ya haukace saboda tashin hankalin da ya shiga.

Wasu ƴan bindiga da ake zargin ƴan ƙungiyar IPOB ne suka kai hari suka kashe mutum 12 da suka ƙunshi mace mai ciki wata tara Harira Jibril da ƴaƴanta huɗu.

Mijin matar kuma mahaifin ƴaƴan dukkanin mata da aka kashe a harin ya shaida wa BBC cewa an kashe matarsa ne da ƴaƴansa a lokacin da suke kan hanyar dawo wa daga ziyarar da ta kai, tare da ƴaƴanta a yankin Orumba ta arewa a jihar Anambra.

“Na shiga tashin hankali, saura kaɗan na haukace – kamar an saka ni cikin wuta, haka nake ji saboda zafin da nake ji,” in ji Jibril Ahmed mijin matar da aka kashe da kuma ƴaƴansa huɗu.

“Yanzu ina zan fara – yaya zan yi aure har na samu ƴaƴan da Allah ya ba ni waɗanda har sun yi nisa da karatu.”

“Yarana suna da basira amma ga shi yanzu irin ɓarnar da aka yi min, kawai na yi tawakalli ga Allah – Allah zai saka min,” in ji shi.

Ya ce yanzu yana koƙarin samun motar da za ta ɗauki gawar matarsa da gawarwakin ƴaƴansa zuwa jihar Adamawa.

Karanta wannan  Iyalan mutanen da akayi garkuwa dasu a jirgin kasa na jihar Kaduna sun kai kuka majalissar wakilai

A cewarsa – yana son a binne gawarsu a jiharsa ta Adamawa.

“An caje ni naira dubu 170 na daukar gawarsu zuwa jihar Adamawa sannan na biya naira dubu 30 a dakin ajiye gawa,” in ji Jibril Ahmed.

Ya ce a cikin satin nan matarsa za ta haihu amma aka kashe ta.

“Iyayen matata sun shiga tashin hankali kuma ina ƙoƙarin tafiya da gawarta domin a binne ta garin iyayenta.”

Ƴan sandan Najeriya sun ce sun kama ƴan bindigar da suka aikata kisan na mutum 12 da suka ƙunshi har da mace mai ciki da ƴaƴanta huɗu.

Ƴan sanda sun ce suna zargin ƴan ƙungiyar Ipob masu fafutikar ɓallewa daga Najeriya ne suka aikata hakan.

Tashin hankali na ƙara ƙaruwa a jihar Anambra musamman hare-haren ƴan bindiga da ake kai wa kusan a kullum.

Lamarin ya ƙara ƙamari a jihar biyo bayan hare-haren da ‘yan bindiga ke kai wa a kullum.

Ko a ƙarshen mako an fille kan wani ɗan majalisar jiha wanda aka tsinci kansa da gawarsa gefen hanya bayan an sace shi a ranar 15 ga watan Mayu.

Kashe-kashen musamman matar da aka kashe da ciki da kuma ƴaƴanta huɗu ya fusata ƴan Najeriya musamman a kafofin sada zumunta na intanet.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Leave a Reply

Your email address will not be published.