Shugaban kasa, Muhammadu Buhari ya bayyana cewa, za’a yi zaben gaskiya a Najeriya dan girmama Abiola.
Shugaban yayi alkawarin gudanar da zaben gaskiya a shakarar 2023 me zuwa.
Yace hakan wata hanyace ta girmama Abiola wanda ya lashe zaben Yuni 12 na shekarar 1993.
Shugaban ya bayyana hakane a ranar Asabar a jawabinsa na ranar Dimokradiyya.