Rikicin na batun barkewa a jihar Kwara, yayin da taron Baptist da Evangelical Church Winning All, ECWA, suka fada wa gwamnatin jihar cewa za su bijire wa sanya hijabi a makarantunsu ta dukkan hanyoyin da suka dace kuma sun nemi a dawo hanzarta dawo masu da makarantunsu.
Dukkanin kungiyoyin kiristocin, a taron manema labarai daban-daban a Ilorin, babban birnin jihar, sun ce ba a tuntube su ba kafin a yanke shawarar.
Muna so mu gargadi gwamnati cewa matakin da take son dauka ta hanyar amincewa da amfani da hijabi ga dukkan makarantun gwamnati da makarantun da ke ba da tallafi a cikin jihar zai haifar da yawan martani, wanda ba wanda zai iya yin hasashensa.
Shugaba Majalisar Baptist na Kwara, Rev Dada, yace wannan matakin gwamnatin jihar ya nuna cewa Musulmai sun fi hakki a kan Kiristocin Jihar.
A karshe yace; ba gwamnatin jihar Kwara ba ko Gwamnatin Tarayya, ba ta isa ta tilasta wa’ ya’yanmu sanya hijabi a makarantunmu ba.