
A shekarar data gabatane Gwamnan jihar Legas Akinwunmi Ambode ya bayyana aniyar gina wasu katafaren tagwayen benaye biyar da zasu kunshi hawa 24 da hawa 31 da hawa 30 da hawa 33 da hawa 24, wadannan benaye dai suna cikin tsarin gina wani sabon gari da ake shirin yi a cikin Legas din wanda aka sawa sun Eko Atlantic City.
Shidai wannan gini na benaye za’a yishine dan zaman mutane , kuma hadin gwigwane tsakanin gwamnati da ‘yan kasuwa, yanzu haka dai rahotanni sun bayyana cewa an kammala guda biyu daga cikin biyar na beyanen kuma abin ya matukar bayar da sha’awa.