fbpx
Saturday, June 10
Shadow

Ko kasan nawane Albashin shugaban kasar Najeriya?: Karanta kasha labari

Shugaban kasar Najeriya: Ya al’amarin yake?
A lokacin da Muhammadu Buhari ya hau kujerar mulki- daya daga cikin shawarwari da ya yanke shine rage yawan kashe-kashen kudi a gwamnati. Hakan bai shafi albashin mataimaka da ma’aikatan gwamnati kawai ba amman harda nashi albashin. Muhammadu Buhari ya yanke yawan albashi da shugaban Najeriya ke karba da 50%. 

Ya yanke albashin mataimakinsa da kashi biyu. Menene albashin shugaban kasar Najeriya a shekara? Ya kai kimanin naira miliyan goma sha hudu. Wannan yana nufin cewa shugaba Muhammadu Buhari yana tafiya da naira miliyan daya a kowani wata. 

Amman kada ku manta cewa shugaban Najeriya yana samun gatanci daga gwamnati. Ya hada da kudin alawas alawas na yau da kullun, kamar kudin wahalhalu (kimanin naira miliyan 1.8) da alawus na dagewa (kimanin naira miliyan 8.8) a shekara.

Sauran alawus-alawus na yau da kullun sun hada da; Kudin Shan man fetur; Kudin amfani; Kudin liyafa; Kudin tsaro; Kudin ma’aikatan gida; Kudin mataimaka na musamman; Kudin mataimaki na sirri. Gwamnati ce take samar da wadannan alawus alawus din. Ba albashi kadai shugaban Najeriya ke karba ba daga gwamnati ba. Yana iya more kudin alawus na rangadi, alawus na kiwon lafiya, alawus na masauki, da alawus na kayan daki. 
hausa.naija.ng

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Talla: Danna nan dan samun gagarumar kyauta

Karanta wannan  Tinubu ya dakatar da gwamnan CBN Emefiele, kuma DSS sun kamashi

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *