fbpx
Friday, July 1
Shadow

Ko Kun San Cewa Wanda Atiku Ya Dauko A Matsayin Mataimaki Ya Taba Ginawa Musulmai Masallaci A Jiharsa Ta Delta?

Ko Kun San Cewa Wanda Atiku Ya Dauko A Matsayin Mataimaki Ya Taba Ginawa Musulmai Masallaci A Jiharsa Ta Delta?

Wannan shi ne Dr ifeanyi OKOWA, mataimakin da dan takarar shugaban kasa a jam’iyyar PDP ya fitar Alh Atiku Abubakar.

Wannan shine katafaren masallacin da Gwamna Ifenyi A okowa ya Gina wa Al’ummar musulmai A jihar sa na Delta, Bai saya Anan ba ya samarwa Yan uwa Hausawa da Fulani muhalli Mai kyau, sannan Yana da commissioner Dan Arewa muhammed inuwa bakari commissioner na ma’adanai na jihar.

Sannan Yana shire tallafi na kudi makudan miliyoyi ko wacce shekara ya baiwa musulmai don su gudanar da shagalin bukukuwan su na sallah yadda ya kamata cikin Jin dadin da walwala, ba’a taba samun report na musgunawa ko tozarci ga Yan Arewa mazaunan jahar ba.

Karanta wannan  Hukumar zabe ta INEC ta karawa masu yin rigistar katin zabe lokaci amma ta gargadi jam'iyyar APC, PDP da dai sauran su

Bugu da Kari Akwai wasu Yan Arewan da ya Basu damar yin karatu kyauta ba tare da sun biya ko sisi ba, kaf a tarihinsa bayada kabilanci ko nuna wariyar yare ko ta addini.

Za’a iya kwatantasa da tsohon ministan sufuri Rotimi Amaechi wurin nuna rashin kabilanci.

Daga Amina Isiyaku

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Leave a Reply

Your email address will not be published.