Korarriyar, fitacciyar jarumar fina-finan Hausa da turanci, Rahama Sadau wadda yanzu haka tana can kasar Cyprus, ta bayyana cewa ta hadu da wani me shirya fina-finan kasar Turkiyya a karin farko, Rahamar ce nan da mutumin a wannan hoton na sama, jarumar wadda dama ta bayyana cewa tana koyon yaren kasar Turkiyyar, da alama, watakila ta fara yin shirin fim acan.
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});
Likafar Rahama Sadau dai nata kara cigaba tun bayan korar da aka mata daga masana’antar fina-finan Hausa sanadiyyar rungumar mawaki Classiq da tayi a wani bidiyon waka da suka fito tare.
A nan Rahamarce a wani shagon sayar da kaya na kasar Cyprus din.
Muna mata fatan Alheri.
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});