fbpx
Friday, August 12
Shadow

Ko sisi bamu biya ‘yan bindiga ba kafin su saki mutane bakwai a wannan makon, cewar me sasanci tsakanin gwamnatin tarayya da ‘yan bindiga

Mai magana da yawun Sheik Ahmad Gumi, Malam Tukur Mamu ya bayyana cewa ko sisi basu biya ‘yan bindiga ba kafin su saki mutane bakawai a wannan makon.

Ya bayyana hakan ne biyo bayan wasu ‘yan jarida da suka bayyana cewa sun biyan naira miliyan 800 kafin aka sako fasinjoji bakwai cikin wa’yanda da aka garkuwa dasu a jirgin kasa.

Amma Mamu wanda ke sasanci tsakanin gwamnati da ‘yan bindiga ya bayyana cewa ko sisi basu biya kuma shi abinda yake yafi karfin kudi sannan ba zai taba shiga harkar da za a bayar da kudi ba.

Leave a Reply

Your email address will not be published.