Shugaba Muhammadu Buhari ya yi Allah-wadai da jerin hare-haren da aka kai waɗanda suka yi sanadin kashe sama da mutum 150 a jihar Filato da ke arewa ta Tsakiyar Najeriya.
A martaninsa na farko bayan kashe-kashen na ranar Lahadi, Shugaba Buhari ya ce ba za a taɓa yafe wa “masu wannan aika-aika ba” kuma “ba za su samu rahama ba”.
Ya dai bayyana lamarin a matsayin hare-haren ta’addanci.
Shugaban na Najeriya ya yi ta’aziyya ga iyalai da dangin mutanen da hare-haren suka shafa.
‘Yan bindiga ne a kan gomman babura suka auka wa mutane da harbe-harbe tare da ƙona ɗumbin gidaje a wasu ƙauyuka aƙalla huɗu cikin ƙaramar hukumar Kanam ta jihar Filato, abin da ya tilastawa ɗaruruwan mutane tserewa da gidajensu.
Ƙauyukan da hare-haren suka shafa sun haɗar da Gyambau da Kukawa da Kyaram da kuma Dungur.
Mafi yawan waɗanda aka kashe, an yi musu jana’izar bai ɗaya a manyan kaburbura daidai lokacin da ake ci gaba da neman wasu ƙarin gawawwaki a dazukan da ke kusa da ƙauyukan.
Da yawan waɗanda hare-haren suka shafa, an kashe su ne lokacin da suka yi ƙoƙarin tserewa.
A kai ɗumbin mutanen da suka jikkata zuwa asibitoci, akasarinsu da raunukan bindiga.
Lamarin na iya zama ɗaya daga cikin hare-hare mafi muni da gungun ‘yan fashin daji suka kai tun bayan fara kashe-kashe da satar mutane don neman kuɗin fansa sama da tsawon shekara goma a arewacin Najeriya.
Gwamnatin Najeriya dai na shan gagarumar suka saboda gazawarta wajen shawo kan hare-haren da ke daɗa ƙazanta duk da tura dubban dakarun sojoji a sassan yankin.
Shugaba Buhari ya ba da umarni ga dakarun tsaro su gano waɗanda suka tafka aika-aikar kashe-kashen baya-bayan nan don gurfanar da su gaban hukunci cikin gaggawa, ya ƙara da cewa ko ta halin ƙaƙa sai an samu zaman lafiya a Najeriya.
Daga BBChausa