fbpx
Sunday, December 4
Shadow

Korar malan jihar Kaduna daga aiki: “Son cin zabe bazai hanani yin abinda ya kamata ba dan nasan wataran Allah zai tambayeni akan shugabancin dana yi”>>Gwamnan jihar Kaduna

Labarin korar malaman makarantar firaimare na jihar kaduna da suka fadi jarabawar ‘yan aji hudu, sanadin haka gwamnan jihar yasha alwashin sai ya koresu daga aiki domin ya maye gurbinsu da wadanda suka cancanta yana kara daukar hankulan mutane a kusan dukkan fadin kasarnan, akan wannan batu gwamnan yayi wasu bayanai masu taba zuciya musamman a gurin masu sukarshi saboda matakin da yake niyyar dauka akan malaman makarantar.

Gwamnan yace kwadayin cin zaben shekarar 2019 da za’ayi nan gaba bazai hana shi yin abinda ya dace ba saboda yasan cewa wataran Allah zai tambayeshi yanda ya gudanar da shugabancin daya bashi.

Gadai abinda gwamnan ya rubuta a dandalinshi na sada zumunta da muhawara da shafin Facebook kamar haka:

“Kuna tunanin inason in fadi zabe ne? A’a bamason mu fadi zabe a 2019 amman son cin zabe ba zai hana mu yin abin da ya dace ba, don wataran Allah zai tambaye ni yadda na gudanar da shugabancin da ya bani.”

Malaman karkashin jagorancin kungiyar gwadago sun gudanar da zanga-zanga inda sukaje majalisar jihar Kaduna wanda har wasu rahotanni suka bayya cewa sunyi fashe-fashen wasu kayayyakin gwamnati dake cikin ginin majalisar.

Karanta wannan  Shaykh mufti Ismail Menk taréda Farfesa Isa Alí Ibrahim (Pantami) a wajén taron zaman lafìya da hadin kai na dunìya 2022 da ké gudana yanzu haka a bírnín tarayya Abuja

Wannan abu daya faru yasa mutane da dama sunyi Allah wadai da abinda malaman sukayi sannan aka rika tambayar cewa “wai irin wadannan malamanne suke koyar da yara a makarantu” to indai hakane basu cancantaba.

Wannan hoton na daya daga cikin malaman daya daga kwalin dake dauke da kalaman cewa” jarrabawa bata nuna ainihin ilimin da mutum ke dashi” ya dauki hankulan mutane, inda da yawa suka bayyana cewa malami be kamata ya rubuta irin wadannan kalamai ba, kuma hakan ya kara tabbatar da cewa malaman basu cancantaba.

Akan batun zanga-zangar gwamnan yace bazata taba hanashi korar malamai ba da yin abinda ya kamata ba kamar yanda dokar aiki ta tanada.

Ga abinda ya rubuta a dandalinshi na shafin Facebook dagane da batun zanga-zangar:

“Ba wata zanga-zanga da za ta hana gwamnati daukan kwararrun malamai, tare da ba malaman da za a sallama hakkokinsu kamar yadda dokar aiki ta tanada”

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Talla: Danna nan dan samun gagarumar kyauta

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *