fbpx
Friday, May 27
Shadow

Korarren kocin Super Eagles ya kai karan kungiyar kwallon kafa ta Najeriya wurin FIFA, ya bukaci a biya shi diyya na dala miliyan guda

Korarren kocin Super Eagles, Rohr ya kai kungiyar kwallon kafa ta Najeriya kara wurin hukumar wasan kwallon kafa ta duniya wato FIFA.

Rohr ya kasance yana horas da kungiyar kwallon kafa ta Nakeriya tun watan oktoba na shekarar 2016 kafin su kore shi a watan disemba na shekarar 2021.

Kocin ya kai Najeriya kara ne don ta kore shi ba bisa ka’ida ba kuma ya bukaci a biya shi diyya na dala miliyan daya duk a cewa ta amince ta cigaba da biyan shi albashi har kwantirakin shi ya kare.

Kuma hukumar FIFA tana gudanar da bincike akan lamarin.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Leave a Reply

Your email address will not be published.