fbpx
Monday, March 1
Shadow

Kotu ta bada umarnin tsare wani yaro da abokansa da ake zargi da yada bidiyon tsiraicin wata yarinya a Sakkwato

Wata Kotun Majistare da ke jihar Sakkwato ta ba da umarnin a tsare wani yaro da abokansa har zuwa 19 ga Oktoba bisa laifin wallafa hoton bidiyon tsiraicin wata yarinya, wanda yayi sanadiyyar fasa auren ta wata.

Aminu Hayatu Tafida, tare da abokansa (wadanda ake zargin) an gurfanar da su a gaban kuliya bisa aikata laifi da suka hada da fyade da kuma yada bidiyon wadda aka yi fyaden don bata suna.

Mai gabatar da kara ASP Samuel Sule ya ce laifukan sun saba wa sashi na bakwai na dokokin hukunta masu laifi na jihar Sokoto, amma wadanda ake zargin duk sun musanta aikata laifin.

Lauyan Tafida, Barista A.Y Abubakar ya yi watsi da zarge-zargen da ake yi wa wanda yake karewa yana mai cewa Rahoton Farko na ‘yan sanda bai fadi karara karar da ke kansa ba.

Lauyan da ke kare sauran mutane ukun da ake zargi Barista Yahaya Gwaza ya ce akwai shaidu kwarara a kan wadanda yake karewa.

Bayan sauraren hujjojin dukkan bangarorin, Babban Alkalin kotun Shu’aibu Ahmad ya dage karar zuwa ranar 19 ga watan Oktoba don ‘yan sanda su shirya akan tuhumar da suke wa wadanda ake zargin.

Ya kuma bayar da umarnin tsare wadanda ake zargin har zuwa ci gaba da shari’ar.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:


×
Kano

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *