fbpx
Friday, July 1
Shadow

Kotu ta buƙaci hukumar kwastam ta biya diyyar naira miliyan 100 ga iyalan mutumin da jami’inta ya harbe

Wata kotun tarayya a jihar Kebbi da ke arewacin Najeriya, ta umarcin Hukumar tsaro ta kwastam da ta biya naira miliyan dari ga iyalan wani mutum da jami’in hukumar ya harbe.

Cikin wata shari’a da ake wa kallon mai wuyar sha’ani, kotun ta kuma umarci Hukumar da ta bayar da hakuri ga al’umma da kuma iyalan wannan mutum.

Mai shari’a Babagana Ashgar ne ya jagoranci zaman kotun wadda ta yi umarnin biyan wannan diyya ta naira miliyan 100 ga iyalan Abdurrahaman Sani Bunza, wanda wani jami’in Hukumar ya kashe a ranar 10 ga watan Nuwambar 2020, a gonarsa.

Ta kuma yi wannan umarni ne bayan da ta ce an ci mutuncin iyalan marigayin an kuma take hakkinsa na rayuwa tare da kawo shi karshe lokacinsa bai yi ba, kamar yadda lauyan iyalansa Umar Aminu Kalgo ya shaida wa BBC.

Karanta wannan  Hotuna:Shugaba Buhari ya gana da shugaban kasar Portugal

Mahaifin marigayin Alhaji Sani Bunza ya ce ba za su taba mantawa da shi ba, saboda mutuwarsa ta girgiza su.

Yayin shari’ar dai bangaren lauyoyin Hukumar kwastam sun kalubalanci hukuncin, tare da bayyana yadda kisan Abdurrahama ya zo musu da tsautsayi, sun ce ana yin wani tashin hanakali ne, a yayin kokarin kwantar da kura tsotsayi ya faɗa kan marigayin.

Abdurrahaman Sani dai ma’aikacin gwamnatin jiha ne kafin ya rasu, ya mutu ya bar mata biyu da ‘ya’ya biyar.

BBChausa.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Leave a Reply

Your email address will not be published.