Hukumar SCID ta maka Oleniju Anthony dan shekara 30 a kotun jihar Legas bayan ya kashe wata mata ‘yar shekara 69 Josephine.
Anthony ya kashe matar ne a jihar Legas bayan sun samu sabani a tsakaninsu amma hukumar bata bayyana abinda ya hadasu fadan ba.
Inda suka bayyana cewa ya shaketa ne har ta fadi ta fara shurawa kafin aka garzaya da ita asibiti inda wa’adinta ya cika a can.
Kotun majistaren dake Yaba ta dage karan izuwa 15 ga watan Nuwamba domin ta yanke shawara akan kai karan babban kotu.