fbpx
Wednesday, August 10
Shadow

Kotu ta daure wani mai safarar giya watanni 8 a gidan gyaran hali a jihar Kano

Wata kotun majastare dake da zamanta a jihar Kano ta daure Kube Bulus watanni 8 a gidan gyaran hali, ko kuma biyan tarar naira 70,000 a sakamakon kamashi da a kai da zafarar barasa.
Kotun dake zaune a Gasau a karamar hukumar Kumbotso ta samu Kube Bulus da laifin safarar giya daga sabon gari zuwa Panshekara dake birnin jihar kano.
Kwamandan hukumar hisba a karamar hukumar kumbotso Gwani Murtala ya shaidawa Hutudole cewa, hukumar ta cafke wanda a ke zargin ne a ranar Juma’a inda kuma ta gabatar da shi a gaban kotu a ranar litinin.
 
Kamar yadda ya shaida mana cewa “Hukumar ta cafke Bulus dauke da barasa a cikin babur mai kafa uku a yankin panshekara.
 
Haka zalika kwamandn ya bayyana cewa “giyar wacce ta kai ta kimanin Naira 400,000 an boye ta ne a cikin babur din a dai-daita sahu ta yadda babu wanda zai gane ta.
 
A cewarsa “Jami’an mu sunyi nasara kama Bulus tare da direban baburin mai suna Emmanuel Peter.” Inji shi
Sai dai kwamandan ya shaida mana cewa hukumar ta saki direban baburin a sakamakon bata same shi da laifin komai ba, hasalima an yaudare shi ta hanyar dora masa dakwan giya a cikin baburin nasa. Kamar yadda kwamandan ya bayyana.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Karanta wannan  Hukumar 'yan sanda ta kori wani jami'inta daga aiki bayan daya lallasa wani mutun da adda

Leave a Reply

Your email address will not be published.