fbpx
Wednesday, May 25
Shadow

Kotu ta daure wasu ma’aikatan banki guda biyu bisa samunsu da laifin satar N2.9m daga asusun wani kwastoma da ya rasu

Mai shari’a Elias Abua na babbar kotun jihar Cross River da ke zamanta a Calabar, jihar Kuros Riba, ya samu wasu tsoffin ma’aikatan banki: Titus Chima Nwankwo da Utibe-Abasi Ifiok George da laifin satar kudi N2,900,000 (Miliyan Biyu, Dubu Dari Tara) Naira kawai) daga asusun wani kwastoman bankin yan kasuwa wanda ya mutu.

An yanke wa Nwankwo da George hukunci a ranar Talata, 26 ga Afrilu, 2022 bayan sun amsa laifuka daban-daban da suka hada da alat din bogi, hada baki, zagon kasa da sata.

Karanta wannan  Yan sanda sun kama wasu da ake zargin ‘yan fashi ne a Bayelsa, sun kwato bindigogi

Mai shari’a Abua ta yanke wa George hukuncin daurin watanni uku a gidan yari tare da zabin tarar N100,000.

Ya kuma yanke wa Nwankwo hukuncin daurin watanni uku tare da zabin biyan tarar N50,000.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Leave a Reply

Your email address will not be published.