Kotun tarayya ta ki amincewa da korafin gwamnan babban bankin Najeriya, Godwin Emefiele na cewa yana son tsayawa takarar shugaban kasa sannan kuma ya ci gana da rike mukaminsa.
Lauyan Emefiele, Mike Ozekhome ne ya shigar da karan inda yake cewa, a baiwa wanda yake karewa damar neman takarar shugaban kasa kuma ya ci gaba da rike mukaminsa.
Saidai mai shari’a Justice Ahmed Mohammed yayi fatali da wannan bukata.