fbpx
Tuesday, August 9
Shadow

Kotu ta mayarwa Gwamnatin Najeriya sama da Miliyan Dari 4 da ake zargin wani tsohon janar din soja da samu bata hanyar halas ba

Babbar kotun gwamnatin tarayya dake da zama a Legas ta mayarwa da gwamnatin Tarayyar kudin da suka kai Naira Miliyan 426.7 data kwace daga Janar John Onimisi Ozigi me ritaya.

 

Me shari’ar Muslim Hassan ya bayyana cewa kotu ta amince da bukatar EFCC na kwace kudin ta mayarwa gwamnati.

 

Ya kara da cewa wanda ake zargi da kamfaninsa sun kasa baiwa kotu dalilin da zai hana mayarwa da gwamnati kudin wanda dukkan alamu sun bayyana cewa bata hanyar halas aka samesu ba.

Karanta wannan  An zargi gwamnatin Zulum da biyan malaman makaranta Albashin Naira Dubu 6

 

Yace shi wanda ake zargi din yana da mukamin Birgedia Janar ne kuma wanda aka kiyasta Albashinshi 750,000 ne dan haka babu wata hujja dake nuna cewa kudin dana samu ta hanyar halas aka samesu.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Leave a Reply

Your email address will not be published.