A ranar Juma’ar da ta gabata ne Babbar Kotun Tarayya da ke Kano ta sallami tsohon ministan harkokin kasashen waje, Aminu Wali tare da wanke shi daga zargin karbar kudin yakin neman zabe na Naira miliyan 950 daga jam’iyyar PDP a lokacin zaben shugaban kasa na 2015.
Hukumar da ke yaki da masu yi wa tattalin arzikin kasa zagon kasa wato EFCC ce ke tuhumar Mista Wali da Mansur Ahmed da aikata laifuka uku wadanda suka hada da karbar kudin yakin neman zabe har Naira miliyan 950 da ake zargin sun karba daga Jam’iyyar PDP a shekarar 2015, lamarin da ya saba wa sashe na 1 na dokar hana safarar kudi ta 2011.
Da yake yanke hukuncin, alkalin kotun Lewis Allagoa ya ce masu gabatar da kara sun gaza gabatar da hujjojinsu ba tare da wata tantama ba.
Don haka ya sallami wadanda ake tuhumar kuma ya barranta dasu.