fbpx
Sunday, May 22
Shadow

Kotu Ta Tisa Ƙeyar Jaruma Mai Kayan Mata Zuwa Gidan Yari

Wata babbar kotu dake zamanta a babban birnin tarayya Abuja, ta aike da shahararriyar mai sayar da kayan matan nan wato Hauwa Sa’idu wacce aka fi sani da Jaruma zuwa gidan Yarin.

Jaruma ta gigita kafar sada zumunta ta Instagram da cika baki kan yadda ta ke da ƙafa da kuma yadda ta san mutane saboda sakin ta da aka yi bayan Ned Nwoko ya sa an kama ta.

Biloniya Ned Nwoko ya sa aka sake cafke mai siyar da kayan matan kan zargi ta da ya ke da cin zarafi a yanar gizo, ɓata masa suna da sauran laifuka da ake zargin ta da su.

Kamar yadda rahotanni suka bayyana, Alkali ya hana lauyan Jaruma belin ta kuma an aike ta gidan yari har zuwa ranar Juma’a, 28 ga watan Janairun 2022.

Idan baku manta ba, a kwanakin baya rikici ya kunno kai tsakanin hamshaƙin ɗan kasuwa Ned Nwoko da Jaruma, bayan da Mista Ned ya saki uwar-gidansa ƴar ƙasar Morocco Laila Charani bayan ya auri jarumar Fina-finai Regina Daniels.

Karanta wannan  Hotunan ziyarar Amaechi a jihar Borno

Faruwar hakan yasa nan da nan Jaruma ta yaɗa cewa haɗin kayan matan da ta bawa amaryarsa Regina ne ya ruɗa shi yasa ya saki uwar-gidansa ƴar ƙasar Marocco Laila Charani.

Sai dai tun a lokacin Mista Ned ya mayarwa da Jaruma kakkausan martani, inda ya bayyana cewar, idan har kayan matan da take sayarwa yana tasiri mai yasa ta kasa riƙe mijinta da shi ta bari har aurenta ya mutu.

Tun a bara ne dai aka fallasa cewa auren Jaruma da Isabor ya mutu har akayi ta cece-kuce.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Leave a Reply

Your email address will not be published.