Wata kotun majistare da ke zamanta a Ilesa a jihar Osun, a ranar Litinin din da ta gabata ta tasa keyar wasu da ake zargin barayi bisa laifin satar na’urar taranfoma da kudinsu ya kai N700,000 a Owa Obokun na Ijeshaland, fadar Oba Adekunle Aromolaran.
Wadanda ake zargin, Owolabi Abimbola mai shekaru 33, Sulaiman Mutiu, 25, Samson Oluwafemi, 25, da sauran su yanzu haka suna fuskantar tuhume-tuhume hudu kan laifin da suka aikata.
A cewar dan sanda mai gabatar da kara, Insfekta Adigun Kehinde, igiyoyin taranfoma da aka sace mallakin IBEDC reshen Ilesa ne.
A hukuncin da ya yanke, alkalin kotun, A.O Awodele, ya dage ci gaba da sauraron karar har zuwa ranar 18 ga watan Mayu, sannan ya bayar da umarnin a ci gaba da tsare wadanda ake kara a hannun ‘yan sanda.