fbpx
Friday, June 9
Shadow

Kotu Ta Tura Wadanda Ake Zargi Da Kashe Deborah Gidan Yari

Daga Aliyu Samba

Rundunar ‘yan sanda ta jihar Sakkwato ta gurfanar da wasu mutane biyu da ake zargi da hannu a kisan daliba mai matakin aji na 2 a Kwalejin Ilimi ta Shehu Shagari da ke Sakkwato, Deborah Samuel da ake zargi da furta kalaman ɓatanci ga Annabi Muhammad Sallallahu alaihi Wasallama cikin wani sakon sautin murya a dandalin sada zumunta na whatsapp.

Wadanda ake zargin, Bilyaminu Aliyu da Aminu Hukunchi wadanda suma daliban kwalejin ne, an gurfanar da su a gaban wata kotun majistare da ke jihar Sakkwato a ranar Litinin.

A cewar rahoton farko na ‘yan sanda, an gurfanar da wadanda ake zargin ne a gaban kuliya sakamakon harin da suka yi wanda ya kai ga halaka dalibar.

Bayan wadanda ake zargin sun ki amsa laifin da ake tuhumar su da su, dan sanda mai shigar da kara, Insifekta Khalil Musa, ya bukaci kotun da ta sanya wata rana domin baiwa ‘yan sanda damar kammala bincike.

Karanta wannan  Lionel Messi zai koma Inter Miami, An yanke shawarar kuma za'a sanar da komawar l shi a cikin sa'o'i masu zuwa

Lauyoyin wadanda ake kara karkashin jagorancin Farfesa Mansur Ibrahim ba su yi adawa da bukatar ba, saidai sun roki kotun da ta bayar da belin wadanda ake kara, inda suka bayyana madigarar su da sashe na 157, 161(a,f) da 164 na kundin shari’ar laifuka ta jihar Sakkwato , da kuma sashe na 36 (5) na Kundin Tsarin Mulkin Tarayyar Najeriya na 1999 da aka yi wa kwaskwarima.

Kotun ta dage sauraron karar zuwa wani lokaci wanda za a sanar da lauyoyin daga baya, sannan ta umurci a tsare wadanda ake tuhuma a gidan gyaran hali na jihar Sakkwato.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Talla: Danna nan dan samun gagarumar kyauta

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *