Wata Babbar Kotun Tarayya dake Abuja (FCT) a ranar Laraba ta umarci kamfanin jirgi na Arik Air ya biya kimanin naira miliyan 10 ga wani fasinja a sakamakon jin kirin tashi da jirgin yayi wanda ya jawa fasinja tsaiko.
Wani fasinja, mai suna Isa Modibbo, wanda ke da cutar ciwan sukari , ya ba da rahoton rasa ganawar sa da likitansa dake zaune a sokoto wanda aka tsara tashin jirgin daga Abuja zuwa sokoto da misalin 10: 30 na safe amma sai jirgin ya tashi da misalin karfe 6 na yamma. a ranar 16 ga watan Disamba 2017.
Rashin gamsuwa da matakin kamfanin jirgin ne yasa Modibbo shigar da kamfanin jirgin saman kara saboda “tauye hakkinsa na dan adam da aikai”.
Da yake yanke hukunci a ranar Laraba, Mai shari’a Danlami Senchi ya ce gazawar kamfanin sufurin jirgin sama na kin cika sharuddan kwangila na jigilar mai kara zuwa Sakkwato daga Abuja a lokacin da aka tsara wanda yake akan jaddawali “babban laifi ne na kwangila da keta hakkin mai kara, tare da tauye hakkin ‘yancin motsawa.
Senchi ya cigaba da cewa bisa gazawar kamfanin jirgin saman, kamfanin zai biya wanda yayi kara kimanin naira miliyan 10.
A karshe mai sharia ya gargadi masu Kamfanin da suna mutunta fasinjojin su.