fbpx
Wednesday, August 10
Shadow

Kotu ta wanke dan Najeriya, Ibrahim daga zargin safarar miyagun kwayoyi a Saudiyya

Wani dan Najeriya Ibrahim Abubakar Ibrahim ya shaki Iskar ‘yanci bayan da kotun kasar Saudiyya ta wankeshi daga zargin safarar miyagun kwayoyi da aka mai.

 

A shekarar 2017 ne jihar Zamfara ta dauki nauyinshi zuwa aikin Hajji, saidai yana sauka a kasar Saudiyya aka kamashi da wannan zargi.

Kotu ta wankeshi da ga zargin a baya amma alkalin ya bukaci a sake masa shari’a. Ma’aikatar kasashen waje ta bayyana cewa gwamnati ce ta shiga maganar shiyasa aka saki Ibrahim.

 

Kuma ta bayyana farin cikinta da wannan lamari inda ta bayyana cewa, jakadan Najeriya a Saudiyyar ya fara shiryawa komowar Ibrahim gida.

Leave a Reply

Your email address will not be published.