fbpx
Friday, March 31
Shadow

Kotu ta yanke wa matashi hukuncin kisa bisa kashe kishiyar mahaifiyarsa a Kano

Wata Babbar Kotun Jiha, mai zaman ta a sakatariyar Audu Bako a Jihar Kano, ƙarƙashin Mai Shari’a Aisha Mahmud, ta yanke wa wani matashi, Sagiru Wada hukuncin kisa ta hanyar rataya bisa kashe kishiyar mahaifiyarsa.

A yayin yanke hukuncin a jiya Laraba, Mai Shari’a ta yi karatun baya, inda kuma ta samu matashin da laifin daddatsa kishiyar mahaifiyarsa da adda, inda ta kuma yanke masa hukuncin kisa, karkashin sashi na 221 na kundin dokar laifuka na Kano.

Kotun ta ce ta gamsu da tuhumar da ake masa bayan samun cikakkun shaidu, ta kuma yanke masa hukuncin kisa ta hanyar rataya.

Tun da fari, an gurfanar da Wada bisa laifin kashe kishiyar mahaifiyarsa, Zainab Dan-Azumi da wata adda shekaru 8 da suka gabata.

Lauyan wanda ake ƙara, Barista Rabi’u Abubakar ya shaida wa kotun cewa matashin bashi da lafiyar ƙwaƙwalwa, amma kotun tai watsi da wannan rokon bisa cikakkun shaidu da tayi amfani da su.

Karanta wannan  Ramadan: Ƴansanda sun kama mutane 14 da zargin aikata fashi da dabanci a Kano 

Lauyan gwamnati, Barista Tijjani Ibrahim ya ce kotu ta yi nazari ta ga babu wani dalili da za a ce yana da motsi a ƙwaƙwalwar sa kuma hakan bai gamsar da ita ba, inda ta yi watsi da rokon.

Shi ma lauyan wanda ake ƙara ya ce za su zauna su yi nazari kuma su ga mataki na gaba da za su ɗauka.

Ali Mandawari, ɗan uwan marigayiyar ne, ya ce sun yi farin ciki da hukuncin kuma gaskiya ta yi halin ta.

Daily Nigerian.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Talla: Danna nan dan samun gagarumar kyauta

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *