fbpx
Thursday, August 18
Shadow

Kotu ta yankewa barawo hukuncin rayuwa a gidan yari bayan ya harbi wani dalibi a jihar Ekiti

Babbar kotun jihar Ekiti ta yankewa wani barawo hukuncin rayuwa a gidan yari bayan yayi kokarin kashe wani dalibi.

Barawon, Babalola Olatomide dan shekara 27 tare da abokansa sun kaiwa daliban farmaki ne a dakinsu shekarar a watan janairu na 2021 inda suka sacewa daya daga cikinsu waya da kuma labtop.

Barayin sun shiga har dakin daliban ne suna neman wani Tosin sai daliban sukace ba Tosin a cikin su, amma duk da haka sai da suka kwace masu waya da Labtop.

Inda daya daga cikin daliban Ajayi ya rike barawon sai ya harbe shi su kuma sauran suka tsere, amma an kama wanda yayi harbin an yanke masa hukuncin rayuwa a gidan yari.

Leave a Reply

Your email address will not be published.