Babbar kotun jiha ta jihar Akwa Ibom dake Uyo ta yankewa wani dan acaba, Anietie Bassey Etim, hukuncin shekaru 20 a gidan yari.
Alkali Gabriel Ettim ya yanke masa hukuncin bayan ya kama shi da laifin yiwa yarinya karama yar shekara 13 fyade.
Dan acabar ya samu damar yiwa yarinyar fyaden ne bayan ta hau babur dinsa da nufin ya kaita anguwa.
Amma sai yayi amfani da damar ya kaita wata tsohuwar coci yake yi mata fyade akai-akai.