fbpx
Wednesday, August 10
Shadow

Kotu ta yankewa janar din bogi hukuncin shekaru bakwai a gidan yari

Kotun jihar Legas dake Ikeja ta yankewa wani sojan bogi hukun shekaru bakwai a gidan yari, watau Hassan Kareem wanda akafi sani da Bolarinwa Abiodun.

Sojan bogi yayi amfani da sunan tsohon shugaban kasa Olusegun Obasanjo wurin damfarar wani dan kasuwa, Bamidele Safiriyu har naira miliyan 266.5.

Sojan bogin ya buga takaddar karya ne yace shugaba Buhari ne ya zabe a cikin wa’yanda ya baiwa mukamin janar saboda haka yana bukatar aron kudin don ya fara aikin nasa.

A watan janairu na wannan shekarar aka kama shi kuma mai shari’a Oluwatoyin Taiwo ya yanke masa hukun shekaru bakwai a gidan yari ba beli sannan an kwace motocinsa da gidansa da bankinsa.

Leave a Reply

Your email address will not be published.