Babbar kotun jihar Ekiti ta yankewa wani mutun dan shekara 49 Ademola Akinola hukun kisa ta fannin rataya bayan ya kashe yayansa.
Hukumar ‘yan sanda tace ya kashe dan ‘uwan nasa ne bayan ya sace masa babur dinsa na Bajaj.
Kuma an fara gurfanar dashi a gaban kulliyan tun shekarar 2020, inda yanzu alkali Ogunmoye ya yanke masa hukunci daidai da abinda ya aikata.