fbpx
Sunday, February 28
Shadow

Kotu Ta Yankewa Tsohon Jami’in SARS Hukuncin Kisa Saboda Kisan Wani Dan kasuwa ya kuma sace masa Naira N.3m

Wata babbar Kotun da ke zaune a Benin, babban birnin jihar Edo, ta yanke wa wani dan sanda da aka sallama hukuncin kisa ta hanyar rataya. Dansandan mai suna Joseph Omotosho, wanda ke aiki tare da rusasshiyar rundunar ‘yan sanda ta musamman da ke yaki da fashi da makami (SARS) ta Jihar Edo.

 

Sauran mutane hudu da aka kama dashi sune Adeleke Adedeji, Abena John, Oniyo Musa da Henry Shobowole, wadanda suka tsere a cikin tagwayen gidajen yari yayin zanga-zangar #EndSars a watan Oktoban da ya gabata, an dakatar da hukuncin nasu.

 

An zarge su da hada baki wajen kisan wani dan kasuwar mai suna Benson Obodeh, a shekarar 2015 kuma an same su da laifukan, akan tuhume-tuhume takwas da suka hada da hada baki da yin sata da kisan kai.

 

Omotosho ya kuma cire N330,000 daga asusun mamacin ta hannun na’ura mai sarrafa kanta (ATM), bayan da ya samu lambobin sirri (PIN) daga Obodeh kafin a kashe shi.

 

Mai shari’a Ohimai Ovbiagele yace hujjojin da aka gabatar akan wanda ake zargin tabbatattu ne saboda wanda ake zargin ya kasa kare Kansa, bisa haka an yake masa hukuncin kisa ta hanyar rataya, amma kuma yana da damar daukaka kara zuwa kotun gaba.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:


×
Kano

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *