fbpx
Monday, August 15
Shadow

Kotu ta yankewa wani jami’in dan sanda hukucin rataya, ji mummunan laifin daya akata

Babbar kotun jihar Rivers dake patakwal ta yankewa sajan James Imanilu hukunci rataya bayan ya kashe wani direban motar haya mai suna David Legbara.

Alkali Elsie Thompson ce ta yanke masa wannan hukuncin bisa shaidun da aka gabatar mata wanda ke nuna cewa tabbas ya aikata laifin da aka tuhumar shi dashi.

Korarren dan sandan ya aikata wannan laifin ne na kashe direban motar hayan a shekarar 2015 inda ya harbe shi da bindiga ya mutu.

Alkalin tace tabbas shine ya aikata wannan laifin bisa shaidun da aka gabatar mata, saboda haka bai kamata a barshi cikin al’umma ba.

Leave a Reply

Your email address will not be published.